Masana'antar Hausa Hip Hop ta yi babban rashi yau.

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

A yau alhamis 18 ga watan Feburerun 2021 ne masana'antar Hausa Hip Hop ta tashi da wani labarin alhini da jimami, bayan ta sanarwa ta fito na rasuwar daya daga cikin matan Hausa Hip Hop kuma jaruma a finafinan Nollywood da kuma finafinan Yarabawa wato "Halimatu Sadiya da aka fi sani da suna Mamo" ta rasu da sanyin asuban yau din nan.

Mawakiyar ta rasu ne a cikin bacci bayan da ta kwanta a daran jiya, bayan jumawa da ta yi ta na rashin lafiya a tsastsaye ba tara da mutane da yawa sun sani ba a masana'antar. Hotunan "Mamo" sun karade shafukan sada zumunta ne irin su Facebook, WhatsApp da Instagram, dauke da kalaman alhini, bakin ciki, mamaki da kuma adduar fatan samun rahman ubangiji bayan tarin yabo da mawakiyar ta yi ta samu daga yan uwa da masoyan ta.

Mamo wacce ta fara finafinai tin a shekarar 2010, ta kasance mawakiya mai ganbarar zamani wato (Rap) da kuma (R&B) inda yan uwanta mawaka da dama su ke mata kirari da "Mace mai kamar maza".

Tini aka yi jana'izar mawakiyar kamar yadda addinin musulinci ya tanada dare kuma da rokan mata addu'ar samun rahma da gafarar ubangiji. Hakika mutuwar mawakiya Mamo ya bar mutane da dama a jihar Kano da ma wasu jihohin cikin mamaki da takaici, kuma za'a juma ba'a manta mawakiyar ba a masana'antar Hausa Hip Hop da irin gudunmawar da ta bayar.

Leave your comment