Ty Shaban ya fara aikin sabuwar film din sa

By Omar Ayuba Isah

Tura wa aboki ta WhatsApp

Tsohon mawaki kuma jarumi sannan mai shiryawa tare da ba da umarni a masana'antar Kannywood "Ty Shaban ya fara aikin wani sabon film din sa mai suna "Gudun gara" a cikin watan nan na faburerun 2021.

Jarumin wanda kwarerren ma'aikacin radio da talabijan ne, wanda a halin yanzu ya ke gabatar da fitaccen shirin nan ta "Dandalin Nishadi" a tashar "Arewa24", mahaifi ne ga daya daga cikin yaran mawaka kuma jarumi wato " Freeboi Shaba".

 

Ty Shaban dai ya wallafa tarin hotuna ne daga fegen daukan film din na "Gudun gara" a shafin sa na Instagram, inda ya ke sanar wa masoyan sa cewa an fara daukan wannan film na shi kuma a cikin hotunan an ga wa su sanannun fuskokin jarumai da ma sabbin jarumai wa dan da za su taka rawa a cikin film din idan ta fito.

Shi kansa jarumin ne ya ke shiryawa a karkashin kwanfanin sa mai suna "Bluesound Multimedia, inda kuma Dan Hausa ya ke ba da umarni. Ty Shaban na daya daga cikin manyan jarumai ma su tarin kwarewa a masana'antar Kannywood duba da shekarun da su ka yi a masana'antar da kuma irin gudunmawar da su ka bayar.

 

Wani abun jan hankali anan shi ne yadda jarumin ya dage a yan shekarun bayan nan wajan fitowa a finafinai manya tare da shirya na sa finafinan shi ma. Mu na dakon sanin lokacin da wannan film zai fito dan sanar da ku labarin fitowar.

Latest News

Umar M. Shareef ya saki sabuwar waka

 Feezy zai saki sabuwar kundin waka.

Amdaz ya na bikin zagayowar ranar haihuwar sa.

Masana'antar Hausa Hip Hop ta yi babban rashi yau.

Arewa Finext da Adam A. Zango sun saki sabuwar bidiyo

Rahama Sadau ta yi bangajiya ga mahalattan bikin dan uwan ta.

Lilin baba na shirin zagayan gidajan radiyo a Arewa.

Leave your comment