Amdaz ya na bikin zagayowar ranar haihuwar sa.

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

Fitaccen mawaki, jarumi kuma marubuci a masana'antar finafinai ta Kannywood "Abdallah Amdaz" ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa a yau din nan, majiyar mu ya samo labarin haka ne daga shafin sadarwa na Instagram din Jarumi Ali Nuhu, inda ya ke wa mawakin fatan alheri tare daura hoton sa a shafin na sa.

Amdaz wanda a yan kwanan nan ne ya kara fashe wa mawakin bayan da ya fito a cikin shahararren film din nan mai suna "Labarina" a matsayin "Excellence", inda ma su kallo da dama su ke yabon irin rawar da mawaki kuma jarumin ya ke takawa a cikin film din.

Amdaz ya rubutu finafinai da dama na Hausa da na turanci tare kuma da sakin wakoki daban daban da su ma su ka yi tashe irin su " Munafiki" da ya fita a shekarun bayan nan. Bayan film din labari na da jarumin ya fito a ciki, akwai finafinan Kannywood da ya fito a ciki irin su "Labarin Amina series", " in search of the king" na jammaje da dai sauran su.

 

Tini mawaka da jarumai da dama su ke ta daura hotunan Amdaz dan taya shi murna da kuma yi ma sa fatan alheri. Amdaz dai na da shafin Instagram da a ka baiwa alamar inganci ta (verified account) wanda ya ke da mabiya dubu dari biyu da yan kai. Muna wa mawakin fatan alheri daga shafin mu na Mdundo Hausa da kuma sauran mutanan da ke bikin zagayowar ranar haihuwar su a mabiyan shafin nan.

Leave your comment