Feezy zai saki sabuwar kundin waka.

By Omar Ayuba Isah

Tura wa aboki ta WhatsApp

Daya daga cikin matasan mawaka ma su basira a fanni daban daban a arewacin Nigeria kuma kani ga fitaccen mawakin Hausa Hip Hop "Dj Ab", wato " Feezy" ya na shirin fitar da sabuwar kundin waka mai suna "Kingdom".

Mawakin ya wallafa wannan sanarwar ne a shafin sa na Instagram da Twitter a cikin makon nan da mu ke ciki, inda ya sanar wa masoyan sa cewa kundin na " Kingdom " ba kamar ko wani irin kundi bane kamar yadda mutane su ke zato, domin kundin ya na kunshe ne da wakoki guda hudu kawai, wadan da aka yi su cikin salo mai daukan hankali tare da kwarerren aiki irin na zamani.

 

Mawakin wanda ya kware a wajan dauka tare da sarrafa fefen bidiyo da kuma wakoki, game da kide kide iri daban daban, ya shiga sahun mawakan da ake wa kallon salon su ya sha banban da na sauran mawakan arewa ma su salon wakar Hip Hop, R & B, Afro Pop da kuma Blues.

In da ake ganin salon sa ya fi kama da na turawa akan na yan Nigeria, wanda ake ganin hakan ne ya sa ba ko wani mai sauraron wakakin Hausa Hip Hop bane yake sauraron wakokin Feezy. Ya na daga cikin yan kan gaba gaba a kungiyar su ta "Yaron North Side" (Y.N.S). Wanda kusan duk kan su yan uwa ne kuma yan gida daya.

 

Feezy bai baiyana hakikanin ranar da zai saki kundin ba, amma ya ilmantar da masoyan sa da dama wadan da ba su san mai karmar (EP) take nifi ba, inda ya daura wani hoton rubutu da ke dauke da bayanin da ke cewa "EP a turance wato (Extended Play), ya na nifin dan gajeren kundin wakoki da bai wuce kwaya hudu zuwa bakwai ba (4 zuwa 6).

Wanda gaba daya bai wuce mintuna 15 zuwa 28 ba. Ya kuma kara da cewa ya na fatan yanzu an fahimce mai kalmar " EP" ta ke nufi. Mu na jiran lokacin da zai sanar da hakikanin ranar da zai saki kundin na sa.

Latest News

Umar M. Shareef ya saki sabuwar waka

 

Amdaz ya na bikin zagayowar ranar haihuwar sa.

Masana'antar Hausa Hip Hop ta yi babban rashi yau.

Arewa Finext da Adam A. Zango sun saki sabuwar bidiyo

Rahama Sadau ta yi bangajiya ga mahalattan bikin dan uwan ta.

Lilin baba na shirin zagayan gidajan radiyo a Arewa.

Leave your comment