Hausa Music Hanny Billy-O, Freeboi Shaban: Yaran mawaka yan na gada.

Picture source: Freeboi Shaban Facebook page

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Waka kamar ragowar sana'aoi ana gado daga mahaifi ko mahaifiya zuwa yaya, ko daga yayye zuwa kanne ko daga kaka zuwa ga jikoki da sauran wadan da ake da alakar jini da shi.

Kan wannan dalilin be yau za mu yi duba ga mawaka biyu daga jihar Kano wadan da yaran mawaka ne yaya kuma ga shahararrun mawaka biyu a masana'antar Hausa Hip Hop da ta Kannywood. Wadan nan mawaka su ne Hanny Billy-O da kuma Freeboi Shaban.

Sayyada Rabi'abu S. Haruna Music: An yi babban rashi a duniyar mawakan yabo.
Hanny Billy-O: kamar yadda sunan mahaifin sa ya nuna, Hanny "Da" ne ga shaharerren mawakin Hausa Hip Hop kuma malami yanzu a makarantar koyan turanci ta Jammaje sannan mai gabatarwa a gidan radio ta Dala Fm 88.5 a garin Kano. Hanny Billy-O ya fara waka tin a shekarun baya, a lokacin da lil Amir marigayi ke raye an yi yayin su biyun a masana'antar Hausa Hip Hop ta jihar Kano, duba da yadda su ke kananan yara amma cike da baiwa da basira mai burgewa matuka ga masoyan wakokin Hausa Hip Hop. Hanny Billy-O ya yi wakoki da dama na audio irin su "Byebye" "Ya kamata" "Mai abu biyun nan" da dai sauran su.

Mawaki Deezell ya fitar da sabuwar waka


Freeboi Shaban: wannan yaran matashin mawaki kamar yadda a ka sani, "Da" ne ga fitaccen mawaki, jarumi kuma mai gabatarwa a telebishan ta Arewa24 wato Ty Shaban, ya kuma gaji mahaifin shi ne shima kamar yadda Hanny ya yi.

Inda kawo yanzu ya yi wakoki da dama hade da fefen bidiyan su, kuma ya fito a finafinai a cikin masana'antar Kannywood, wanda a cikin su har sa sabon fim da mahaifin sa ya shirya domin shi, mai suna "Tauraron boye". Wadan nan yaran mawaka da su ka gaji iyayen su, sun zamo abun koyi ga kananan yara ma su tasowa da kuma sha'awar fara wakoki.

Jaruman biyu da ke kan gaba a jarumai da su ke da mabiya a shafin Instagram

Ziriums ya yi bikin ranar Uwa ta duniya tare da iyayen sa a nan Najeriya

Leave your comment