Sayyada Rabi'abu S. Haruna Music: An yi babban rashi a duniyar mawakan yabo.
19 March 2021
Picture source: Fityanul Islam Facebook page
By Omar Ayuba isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Ayayin da duniyar mawaka ke cigaba da jimamin rasuwar mawakiyar Hausa Hip Hop yar jihar Kano Mamo Oosha, da kuma mawakin Hausa Hip Hop dan garin Abuja AybeeWon wanda wa su su ka kashe shi a kusa da gidan sa a garin Abuja, anan ma dai masana'antar mawaka ta sake wayan gari da wani babban rashin daya daga cikin manyan mawakan ta da duniya ke alfahari da su a bangaran mawakan yabo na manzan Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi.
Jaruman biyu da ke kan gaba a jarumai da su ke da mabiya a shafin Instagram
A jiya talata 16 ga watan Maris ta 2021 ne, aka tashi da labarin rasuwar tsohuwar mawakiyar begen nan yar jihar Kano wacce aka sani da "Sayyada Rabi'abu S. Haruna. Wannan labarin rasuwar ta ya fito ne kai tsaye daga shafin nan ta mabiyan darikar " Tijjaniya" a Najeriya wato "Fityanul Islam" a Facebook. Tare da sanarwar cewa tini aka riga aka yi jana'izar ta kamar yadda addinin islama ya tanadar.
Marigayiyar ta yi fice sosai a fanin wakokin yabo na addini kamar yadda marigayi Umar Abdullaziz "Fadar Bege", Marigayi Rabiu Usman Baba Marigayi "Bashir Tashe" da irin su Dan dogare, Bashir Dan Musa, Dan dago da dai sauran su.
Ziriums ya yi bikin ranar Uwa ta duniya tare da iyayen sa a nan Najeriya
Wa su daga cikin wakokin da marigayiyar ta sanu da su a duniya sun hadar da
Na yi dace
Sayyidin Nasi
Da dai sauran su.
Dubunnan masoyan ta ne su ka cike kafafan sada zumunta daban daban da sakonnin jimami da na ta'aziyar ta. Yayin da kuma wa su da dama ke sanya wakokin ta a shafukan su na sada zumunta.
Muna taya iyalan ta da masoyan ta da kuma daukacin mawakan yabo na kasar Hausa gabaki daya ta'aziya da alhinin wannan babban rashi da aka yi na Sayyada Rabi'atu S. Haruna a jihar Kano.
Leave your comment