Mawaki Deezell ya fitar da sabuwar waka
17 March 2021
Picture source: Deezell official Instagram account
By Omar Ayuba Isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jihar Kamo mazaunin kasar Amurika Deezell ya saki sabuwar wakar sa mai taken "No Girlfriend" yau talata 16 ga watan Maris 2021 a man'hajojin sauke wakoki mabanbanta.
Wakar "No Girlfriend" da ke nifin "Babu Budurwa" a hausance, waka ce ta hadaka tsakanin mawaka bakwai daga bangarori daban daban daga Arewacin Najeriya hade da shi kan sa mawaki Deezell din wanda ya zo daga kasar Amurika dan wannan aikin wakar "No Girlfriend" da aka yi a jihar Kaduna a karkashin jagorancin mawaki kuma mai bada umarni a bidiyon waka wato Feezy.
Mawakan da Deezell ya gaiyato kan wannan wakar su ne Lil Prince daga Kaduna, Cdeeq da Triple D daga kano, Mr 442 daga garin Zaria, Boyskiddo daga sakwato sai Lxvee daga Kaduna shima, sannan da shi kan sa mai gaiya mai aiki wato Deezell daga kasar Amurika.
Tin kafin fitowar wannan wakar ne masoya da mabiya wakokin Hausa Hip Hop daga jihohi daban daban ke nuna farin cikin su da wannan wakar ta hada ka irin ta na farko a cikin wannan sabuwar shekarar, musanman jihohin da akwai mawakin su a cikin wannan sabon aikin na mawaki Deezell.
Ai saki sabuwar wakar ne kwanaki kadan da komawar mawaki Deezell kasar Amurika inda ya ke da zama, kuma wannan shi ne aikin Deezell na biyu da ya fitar a sabuwar shekarar nan tin bayan da ya saki wakar "Duk abun da zai faru ya faru" ta mawaka goma sha shida (16) da ya gaiyato su cikin wannan wakar ta hadaka.
Related Photo *
Leave your comment