Jaruman biyu da ke kan gaba a jarumai da su ke da mabiya a shafin Instagram
17 March 2021
Picture source Nadubi Naija Instagram account
By Omar Ayuba Isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
A cikin shafukan sada zumunci mabanbanta da ake da su a duniya a halin yanzu, shafin sadarwa ta Instagram na daya daga cikin manya na sahun gaba a tarin masu anfani da shi a fadin duniya. Kuma hakan ya sanya mawaka, Jaruman fim, yan siyasa, yan kwallon kafa da na hannu, yan kasuwa manya da kwanfanunnuka har ma da masu sana'ar hannu iri daban daban.
Wanda wannan tasiri da kafar Instagram ke da shi ne, ya sa ma su masoya musan man yan fim din Kannywood su ka zabi su yi anfani da wannan kafa wajan saduwa tare da tallata basiyar su da harkokin su ga dubunnan masoyan su. Kuma wa su daga cikin wadan nan jaruman su na da masoya miliyoyi a shafin su na Instagram.
Wannan dalilin ne ya sa mu ka yi duba ga masana'antar Kannywood dan mu ga wadan ne jarumai ne ma su masoya fiye da miliyan daya, kuma binciken mu ya zakulo mana jarumai biyu da su ne kadai su ke da mabiya a shafin Instagram fiye da miliyan daya.
A jarumai maza, jarumi Ali Nuhu ne ya ke da mabiya a shafin Instagram fiye da miliyan daya, inda jarumin ke da mabiya mutun miliyan biyu da dubu dari biyu da yan dauriya (2.2 million followers). Inda kuma jarumin ya ke bin mutun dubu uku da dari uku da ashirin da biyu (3,322 following). Yayin da kuma jarumin ya wallafa hotuna dubu goma sha biyu da dari bakwai (12.7K post).
A bangaran mata kuwa, jaruma Rahma Sadau ce kadai mai mabiya a shafin Instagram fiye da miliyan daya, inda jarumar ta ke da mabiya mutun miliyan biyu da dubu dari hudu da yan dauriya (2.4 million followers), inda ita jarumar kuwa ke bin mutane dari hudu da saba'in da daya (471 following) a yayin da kuma ta wallafa hotuna dubu daya da dari biyar da saba'in (1570 post).
Wadan nan jarumai biya hallau dai na da mabiya dubun ne a shafukan su na Twitter kuma su biyun ne su ka fi kowa a cikin masana'antar Kannywood samun kwangilan jakadancin manyan kwanfanunnuwa ciki da wajan Arewacin Najeriya.
Leave your comment