Ziriums ya yi bikin ranar Uwa ta duniya tare da iyayen sa a nan Najeriya

Picture source: Ziriums Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Dan jarida, mawaki, tsohon makadi kuma mazaunin kasar Amurika Naziru Hausawa da aka fi sani da Ziriums ya dawo Najeriya daga kasar Amurika inda ya ke da zama dan taya murnar bikin ranar Uwa ta duniya da aka gudanar a ranar ladadin nan da ta gabata 14 ga watan Maris 2021.


Mawaki ziriums wanda shi ne shugaban gidan radio ta Sarewa radio ta online, wanda ke gudanar da aiyukan ta daga shalkwatar ta da ke kasar Amurika a jihar Washington DC da kuma kasar Jamus inda daga nan ma ake gabatar da shiryeshirye daban daban a radiyan. Ya shigo kasar Najeriya ne a yan kwanakin nan dan ganin gida kamar yadda ya saba a baya, sai dai wannan karon zuwan ya sha banban da na da.

Domin a wannan karon mawakin ya yi bikin ranar Uwa ta duniya tare da iyayen sa a jihar Kano inda nan ne asalin mawakin kafin komawar sa kasar Amurika da aiki.

Mawakin ya wallafa hotunan sa tare da iyayen sa ne a shafukan sa na sada zumunta tare da rubutun yabo gare su da kuma fatan alheri gare su.


Mawaka da dama ne su ka shiga jerin ma su taya Mahaifiyar su murnar wannan rana ta musanman da ake ware wa iyaye mata na duniya gaba daya. Kuma ziriums na daga cikin manyan mawaka da su ka shiga wannan biki.

Leave your comment