Yau Jarumi Ali Nuhu ya ke bikin ranar zagayowar haihuwar sa.

Courtesy Ali Nuhu's Page Instagram

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen jarumi, mai bada umarni kuma daya daga cikin jigajigai a masana'antar Kannywood Ali Muhammad Nuhu da aka fi sani da (Ali Nuhu) ya na bikin zagayowar ranar haihuwar sa a yau alhamis, 15 ga watan Maris ta shekarar 2021.


Jarumi Ali Nuhu wanda shi ne shugaba kuma jagora a kwamfanin sa na FKD Production da ke garin Kano, kuma babban jarumi a masana'antar fim ta Nollywood da ke kuduncin kasan nan. Kuma ahalin yanzu wanda ya baiwa sana'ar kayan sawa wato harkar Boutique lokaci ban da fim da duniya ta fi sanin mawakin da shi.

Tin a daran jiya lahadi ne jarumai da mawakan masana'antar Kannywood su ka fara dauka hotunan Ali Nuhu a shafukan su na sada zumunci daban daban dan taya shi murna da zagayowar ranar haihuwar sa. Jarumi Ali Nuhu wanda ya fara finafinan Kannywood tin a shekarar 1999 izuwa yanzu, ya yi finafinai daban daban wadan da su ka karbu a duniya, kamar yadda finafinan sa na Nollywood su ka karbu tin bayan da ya fito a fim din "Sitanda" a matsayin jarumi sabo a masana'antar ta Nollywood.

Mawaki Umar MB ya fitar da sabuwar kundin waka

Jarumin wanda ya ke da mabiya sama da mutane miliyan biyu a shafin sa na Instagram ya na daga cikin manyan jarumai a masana'antar Kannywood da su ka fi kowa samun jakadanci daga kwamfaninnika manya da ke arewaci da kudancin kasan nan har ma da na kasashen waje.

Kuma kamar yadda wa su ke masa inkiya da sarki, hakika jarumi Ali Nuhu ya kai matakin da ba ko wani jarumi ba ne ya kai a masana'antar ta Kannywood, idan a ka yi la'akari da nasarorin sa, cigaba da ya samu da wanda ya kawo masana'antar. Kuma Ali Nuhu madubin dubawa ne agurin jarumai ma su tasowa da dama.

 

Masoyan Hamisu Breaker sun kai mutun miliyan daya a Instagram

Ana aikin wani sabon fim mai dogon zango irin sa na farko a Kannywood

Deezell ya baiyana sunayen mawakan da yake shirin dagawa a cikin sabuwar aikin da zai fitar.

Mawaki Lilin Baba zai fitar da sabuwar fim

Masana'antar Hausa Hip Hop ta sake babban rashi na wani mawakin

AleeGee ya taya jaruma Gabon murnar ranar mata ta duniya.

Leave your comment