Kamar yadda ya yi alkawari, M-kay ya fitar da fefen bidiyon sa yau juma'a 5 ga watan 3

Photo source: M-Kay Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Join Mdundo's Telegram Channel

Sanannan mawaki kuma kwararren mai daukan hoto "M-kay" ya fitar da sabuwar fefen bidiyan wakar "Nobody" a yau din nan biyar ga watan uku shekarar 2021 . Wannan sanarwar ta fito ne daga mawakin da kan sa ta shafikan sa na Instagram da Facebook, a yau juma'a dazun nan da rana. Inda ya yi masoyan sa albishir da fitowar wannan wakar a ranar juma'a kamar yadda ya yi alkawari.

Idan ba'a manta ba, a ranar 1 ga watan biyu ne na shekarar 2021, M-kay ya saki audio din wakar "Nobody" a shafukan sada zumunta. Wanda a cikin kwanaki uku kachal ne yan mata sama da hamsin (50) su ka dinga yi wa wakar bidiyo challenge a shafukan su. Wanda hakan ya sanya mawakin zuwa jihar Abuja dan yin aikin bidiyon wakar, inda kwararran mai bada umarnin nan Ahmadi ya yi aikin bidiyan tare da editing, kawo yanzu dai tini mawakin ya wallafa wannan waka a YouTube, Instagram da Facebook dan masoyan sa su kalli irin bajinyar da ya yi a cikin wannan fefen bidiyan.


M-kay wanda daya ne daga makusantan shahararan jagoran Hausa Hip Hop Billy-O, mawaki ne mai salon wakokin Rap, R & B, Reggae da ma salon Rauji wato nanaye idan ya so. Har izuwa yanzu tin bayan kammala aikin bidiyan, M-kay na cigaba da zama a garin na Abuja tin barin sa jihar sa na asali wato jihar Kano kamar yadda mu ka sheda mu ku a kwanakin baya.

Masoyan sa su na cigaba da baiyana farin cikin su da wannan fefen bidiyan tare da baiyana ra'ayin su akan yadda bidiyan ya kasance bayan da ta fito. Wakar "Zainabu" ita ce wakar M-kay ta karshe a shekarar da mu ka yi bankwana da shi, wace su ka yi tare da Mister Ladagoma da kuma Uniquepikin. M-kay na daga cikin mawakan DA ba su fiye sakin wakoki da yawa ba sai dai jifa jifa, amma kuma su kan juma ana yayin su idan ya fitar.

Top Stories

Ali Nuhu ya fito a cikin wani sabon fim da ake dauka a halin yanzu.

 

Isah Ayagi ya fara tallata sabon kundin sa.

Burna Boy Featured in Justin Bieber's Upcoming Album 'Justice'

Top Trending New Naija Music Videos to Watch This Week

Latest Sinach Songs: Sinach Drops New Song 'Beautiful' Featuring Nathaniel Bassey

Billy-O Ya Saki Sabon Bidiyo Na Barko Bayan shekaru: "I Love You"

Download Rema: Another Banger! ‘Bounce’, Rema Releases New Song (LYRICS)

Hussaini Danko na shirin sakin sabuwar waka

Leave your comment