Hanyoyi 6 da wakokin ka zasu shahara a dandalin TikTok

Photo credit: Freepik

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

TikTok wani dandalin manhajar yada bidiyo ne wanda aka kirkire shi a shekarar 2016. Kamfanin ByteDance ya zama daya daga cikin manhajar da ake rababi a duniya. Manhajar tana gurbi na bakwai a cikin jerin manhajojin dandalin sada zumunci da aka fi amfani da su a duniya da yawan masu amfani ya kai kimanin miliyan 689. 

Manhajar na da hanyar samun kudaden shiga ta wata tsarin da aka kirkiro mai sunan TikTok Creators Fund (Asusun Mawallafa na TikTok) inda mawallafa wanda shekarun su ya haura 18, kuma suna da mabiya sama da dubu 10, sannan suna iya samun masu kallo har kimanin dubu 100 bayan kwanaki 30 zasu iya samun kudaden shigowa daga kan dandalin na TikTok. 

Fitattun Wakokin Arewa Guda 7 Agusta 2021

Bayan da manhajar ta samu karbuwa, mawaka da masu talla suka rungumi wannan daman ta hanyar amfani da ita wurin tallata wakokin su domin ta kara bunkasa. 

TikTok ya baiwa masu wallafa ayukan su daman sarrafa wakoki, bidiyoyi da dora murya a kan ayukan wasu mawallafa, wata fasahar da wasu shafukan sada zumunci irin su Snapchat da Instagram suke kokarin su ma su aiwatar a kan shafin dandalin nasu. 

Wakoki da dama sun zama bakandamiya sanadiyar TikTok sannan kuwa tambayar da ta rage ga shi mawaki shine ta yaya zai iya amfani da wannan daman domin wakar sa ta samu karbuwa a kan shafin. Ku cigaba da karanta wannan jawabin domin samun satar amsa yanda wakokin ku zasu samu bunkasa a kan dandalin TikTok. 

Fitattun record labels 5 dake kasar Najeriya

- Bidiyo mai daukar hankali: Abu na daya shine fitowa da bidiyo mai daukar hankali a kan TikTok. Abubuwan da ya kamata wakar ka ta kunsa shine sauti mai daukar hankali sannan da aikin da aka nuna bajinta a cikin ta a lokacin da ake sarrafa wakar. Sannan ka tabbatar da cewa amshin wakar mutane zasu iya rike ta cikin sauki da kuma baitukan wakar, mutane zasu iya kawo su cikin sauki ba tare da wahala ba. Daya daga cikin wadannan abubuwan da muka lissafa zai iya janyo wakar ku ta samu karbuwa kan dandalin na TikTok amma ka tabbatar da  cewa ka cike kusan duk gurbin da mika lissafo a nan. 

- Na biyu shine ka saka gasa na musamman: Ka fito da wani abu da zai bambanta wakar ka da sauran wakoki ta hanyar saka gasa. TikTok dandali ne wanda wasannin gasa suke samun tasiri. Fitowa da gasa kala-kala kuma wanda zai dauki hankalin jamma'a zai bai wa masu amfani da manhajar daman uin tsale kan wakar ka sannan wakar ka ta samu karbuwa har ta zama abun yayi a kan dandalin. 

- Hadin gwuiwa: domin wakar ka ta shahara a kan dandalin, yana da kyau ka yi hadin gwuiwa da fitattun gwanayen da suka shahara a kan dandalin na TikTok. Idan wadanda suka yi shura a kan dandalin suka yi amfani da wakar ka a kan shafin su ko kuwa suka shiga gasar da ka saka, wannan zai iya tunzura mabiyan su su kwaikwaye su har su shiga gasar ta ka sanadiyar gwanayen nasu. 

- Dora bidiyoyi hade da wakar ka: Saka ýan uwa da abokan arziki su dora bidiyoyin ka hade da wakar ka yana taimakawa sosai wurin samun karbuwa da shaharewa a kan dandalin. Ba kowa bane suke da daman samun hadin gwuiwa da shahararun masu amfani da manhajar ba saboda yanayin rayuwa amma wannan wata dama ce da zaka iya amfani da shi cikin sauki. Sannan ko da wakar ka ba a saka gasa a kan ta ba, dora wakokin ka na bidiyo a kai a kai yana taimakawa kwarai da gaske. Bidiyoyi masu dauke da sakon tausayi ko barkwanci suna saurin yaduwa a kan dandalin na TikTok. 

Yanda dakatar da Twitter ya janyo tsaiko ga harkokin mawakan Najeriya da masana'antar

-Shiga gasar da ake yayi a wannan lokacin: fitowa da gasar ta ka abune mai kyau amma ya kamata kai ma ka shiga gasar da ake yayi a wannan lokacin. Wannan dana ce wanda zai kara bunkasa shafin ka sannan ka cimma wasu burin naka. A lokacin da aka ziyarci shafin naka domin kallon bidiyon gasar da ka shiga na wasu, mutane zasu samu daman kallon sauran ayukan ka wanda zata iya fashewa idan ka ci sa'a. 

- Yin amfani da alamar #: kusan duk shafukan sada zumunci sun rungumi amfani da wannan alamar kwando ko tsani na # saboda samun sauki wurin neman ayukan su a saukake ba tare da wata wahala ba. Alamar ta # na TikTok wurin amfani kusan daya ne da sauran alamar da ake amfani da su a kan Instagram, Twitter da dai sauran su. Ya taimakawa kwarai da gaske idan ana neman ayukan ka cikin sauki idan har ka cigaba da jajircewa wurin amfani da alamar ta #.

Leave your comment