Yanda dakatar da Twitter ya janyo tsaiko ga harkokin mawakan Najeriya da masana'antar

Photo credit: Getty image

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

A ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni, 2021 gwamnatin tarayya ta dakatar da Twitter a kasar ta Najeriya. 

Labarin dakatarwar ya tada cece-kuce tsakanin kungiyoyi da masana daban-daban musamman manyan mawaka da kungiyoyi masu neman yancin dan Adam wadanda suka tayar da kashin baya game da yunkurin gwamnati kan wannan dokar. 

Bayan kawo iyaka ga kalaman batanci da matsi ga tartalin arzikin kasar, haramta amfani da Twitter ya janyo matsaloli da tasgaro cikin al'amurorin da suka shafi masana'antar waka a wannan lokaci. 

Fitattun record labels 5 dake kasar Najeriya

Duba da yanda kimiyar sadarwa na kara bunkasa, musamman a yankin na Afirka, kafafan sada zumunci na taka muhimmiyar rawa duba da cewa mawaka da dama na amfani da wannan kafa wajen tallata hajar su ga duniya. 

Sau dayawa, mawakin Najeriya kan sanar da fitowar sabon aikin su ko bidiyo ko sauti ta hanyar amfani da kafafan sada zumunci - amma kash, abun yanzu da wuya duba da wannan dokar da aka kafa. 

A wannan karnin, mawaka da dama na samun kudadan shiga ne ta hanyar streaming ko kuwa sauraron wakoki kai tsaye, ko kuwa ta hanyar kallo amma duba da wannan dokar, tabbas za a samu akasi wurin samun kudadan shiga saboda mawaka bazasu samu daman sanar da masoyan su kan fitowar sabbin ayukan su ba ta hanyar amfani da dandalin shafin ta Twitter duba da cewa mawakan na da tarin dumbin masoya wadanda mabiyan su ne. 

Wasu mawakan suna na da yarjejeniya da manyan kamfanoni a yayin da wasu mawakan jakadun su ne. Duba da cewa a kan biya mawakan makudan kudade domin a tallata hajarsu a kan shafin mawakan, an samu akasi wurin samun kudaden shigowa ga mawakan duba da dakatarwar da aka tsayar. 

An nada Sojaboy a mazaunin Yarima

Masu saurarar wakoki su ma suna fama da irin rashin nasu kuwa. Na farko shine an bar su a baya game da abubuwan dake tafe da gwanayen mawakan nasu ta hanyoyin fida sabbin wakoki, bidiyoyi, kundin fefen da ma wasu al'amurorin da suka shafi gwanayen nasu. 

Kaman mawakan, dandalin shafin wakoki suna dogaro da dandalin shafin sada zumunci wurin tallata wakoki irin su Twitter domin masu sayan wakoki su san da sabin wakokin da aka saka. Tabbas yanzu wannan hanyar a toshe take saboda wannan dokar. 

Hamisu Breaker zai saki kundin fefen sa ranar Yuli 21

Mawaka masu tasowa a da suna dogaro da shafin na Twitter domin a san da su. Amma yanzu, an mai da agogon hannu baya saboda ba lallai bane a san dasu. Fitattun mawaka irin su Mayorkun da Reekado Banks sun shahara ne ta hanyar Twitter wanda ya janyo suka samu kwantiragi da alheri mai dumbin yawa ta hanyar wakokin su.  Da wannan dokar da aka sa, mawaka wadanda gwanaye ne cikin duhu baza su samu daman da Twitter take dauke da ita ba wurin tallata kan su domin duniya ta san dasu. 

Ko da dai wasu yan Najeriya na amfani da vpn wurin samun daman amfani da shafin na Twitter, ba ko wanne dan kasa ne yake da wannan daman ba. Tabbas an samu tasgaro da babban gibi a kan harkokin mawaka da masana'antar wakar a halin yanzu. Ko za a samu wani mafita, lokaci ne zai tabbatar da hakan.

Leave your comment