Hamisu Breaker zai saki kundin fefen sa ranar Yuli 21

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Mashahurin mawakin da ludayin sa ke kan dawo a harkar waka irin salon rauji a halin yanzu wato Hamisu Breaker ya saki hoton dake dauke da jerin kundin wakokin da zai saka. 

Ya bayyana hakan ne a shafin sa na sada zumunci bayan da ya saki hoton. Ya kara da cewa "alkhairi insha Allah zai zo muku ranar laraba 21 ga watan July. Ya Allah ka hada mu da alkhairi. Ameen. 

Fitattun record labels 5 dake kasar Najeriya

Kundin fefen sa zai saka mai taken "ALKHAIRI" na kunshe ne da wakoki goma sha hudu (14) da kuma kyautan waka guda. Yawancin wakokin da aka bugu sun fito ne daga hannun Kasheepu. Duba da irin yanayin salon wakokin sa, tabbas wakokin soyayya sun rinjaye kundin fefen aikin.

Hamisu Breaker jarumin mawaki ne wanda ya saki ayuka da dama. Ya saki wakar Sai da Ke wanda a halin yanzu wakar ta samu sama da  masu kallo dubu dari shida da uku (603K views).

Leave your comment