Fitattun record labels 5 dake kasar Najeriya

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Duk wani burin mawaki ko mai tashe ko kuwa mai tasowa shine ya sami record label wand za ta dauki nauyin harkokin sa wanda ya shafi sana’ar san a waka.

Sanin kowa ne cewa harkar waka na da matukar wahala domin babban kalubalen da mawaka ke fuskanta shine rashin ishashen kudin da zasu aiwatar da ayyukan su. 

Ina zama dan yin tunani a kan menene so, inji Hamisu Breaker

Record labels su ke da hannu mai maiko a wannan harkar domin  su ne kashin bayan ko wane babban mawaki. Su ke da daman tallata mawaki, daukan duk nauyin tallata hajar sa da kuma kula da shi a cikin harkar baki daya. 

Wannan sune jerin manyan record labels wanda ake ji da su a halin yanzu a kasar Najeriya kuma basu gaza a harkokin su ba. 

MAVINS RECORD 

Don Jazzy wanda asalin sunan sa …… shine shugaban wannan kamfanin. An samo wannan kamfanin ne bayan rabuwar Don Jazzy da kungiyar Mo’hits. Wannan record label na takama da manyan mawaka irin su Tiwa Savage, Korede Bello, Johnny Drille, Ladipoe, DNA twins da kuma sabon shiga Rema. Sun taka babbar rawa a wajen gina wadannan manyan mawaka. 

DMW (DAVIDO MUSIC WORLDWIDE) 

Davido shine wanda ya fara hada wannan kamfanin a shekarar 2016, a yayin da ya dau nauyin Mayorkun da Dremo a cikin harkar. Record label din ya su daman rike mawaka masu tasowa irin su Idowest, Yonda, Peruzzi da dai sauran su. 

Deezell zai saki sabon fefen mixtape mai taken Vault

DMW sun yi matukar kokari wajen bunkasa harkokin su da kuma samun karbuwa a cikin kankanin lokaci, kuma sun kokarta wajen daga likaffan mawakan dake karkashin ta. Ana alwashin cewa wannan record label it ace ya dace da duk wani mawaki mai tasowa a halin yanzu a kasar Najeriya. 

CHOCOLATE CITY MUSIC 

Tun lokacin da aka kafa kamfanin, Chakulate City Music sun haifar da manyan maka wadanda suka yi fice a harkar har da daya daga cikin masu shugabantar kamfanin, M.I Abaga. Chakulate City Music su ke da hannu wajen nasarar manyan mawakar da ke cikin ta irin su Jesse Jagz, Ice Prince, Brymo, Victoria Kimani da dai sauran su. 

A kwanakin nan ne suka rantama hannu da kamfanin Warner Music Group dake can nahiyar tura a inda suke shirye-shirye wajen ganin an inganta sana’ar waka a kasar Najeriya. 

A halin yanzu dai, Blackbonez shine fittacen mawakin dake jan ragamar record label din Chocolate city.  Shine dai wanda tauraron sa ke haskawa. 

YBNL 

Yahoo Boy No Laptop YBNL wani record label ne wanda Olamide ya kafa bayan murabus da yayi daga Coded Tunes. Mawakin ya gina kamfanin ne da tubalin karfe a yayin da yay aye mawaka da dama a karkashin label din. 

YBNL sun yaye mawaka irin su Lil Kesh, Victoh, Adekunle Gold, Chinko Ekun. Akwai irin su Fireboy DML, Lyta, Picazo Rhap da dai sauran su.

STARBOY ENTERTAINMENT 

Shugaban wannan kamfanin shine fitaccen mawaki mai sunan Whizkid, Starboy Entertainment yana daya daga cikin manyan record labels wanda ake ji da su. Kamfanin ya sum daman daga likaffar mawaka irin su  L.A.X, Maleek Berry, Mr. Eazi, Efya da dai sauran su wadanda suka yi fice a harkar. A halin yanzu, an samu wani sabon shiga mai sunan Terri wanda ya rantama wa kamfanin hannu a kwanakin nan.

Leave your comment