Deezell zai saki sabon fefen mixtape mai taken Vault

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Shahararen mawaki Ibrahim wanda aka fi sanin sa da lakabin Deezell zai saki sabon fefen mixtape mai taken Vault.

Deezell wanda a halin yanzu mazaunin kasar Amurka ne ya bayyana cewa zai saki kundin fefen ne a shafin sa na kan Instagram.

Amdaz ya saki sabuwar waka

A cewar sa "Na yanke hukuncin sakin wasu wakoki na wadanda na rera amma ban sake su ba shekaru takwas da suka shude. Saboda haka, ku saurare su lafiya".

Deezell ya saki wakoki da dama irin su Girma, Ba ruwan mu da haters, Ojoro, da dai sauran su.

Mawaki 442 ya zaki sabuwar waka

Deezell dai ya yi ayuka da shahararun mawakan salon Hip-hop irin su Classiq, DJ AB, Morell, Nomiis Gee, Kheengz, BOC Madaki da dai sauran su.

Leave your comment