Amdaz ya saki sabuwar waka

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren jarumi, marubuci, mawaki kuma mai bada umarni a masana'antar shirye finafinai ta Kannywood "Amdaz" ya saki sabuwar waka mai taken "Yar Balbela" a cikin makon daya gabata na karshen watan Mayu ta shekarar 2021.

Sals Fateetee sun yi waka tare da Pheno B dan kasar Nijar

Amdaz din ne ya sanar da hakan ta shafin sa na instagram, inda ya sheda wa mabiyan sa cewa ya saki sabuwar waka kuma tini ta fita a duk wani manhajar sauke waka a duniya da ake anfani da su. Ya kuma samu masoyan sa da dama wadanda su ka bashi goyan baya ta hanyar hawa wannan wakar su na mata bidiyo daga gari daban daban.

Za A Kawo Karshen Gasar Da Rarara Ya Saka

Amdaz wanda ya kware a wajan rubutun finafinai a Kannywood, kuma yake taka rawa matuka a cikin finafinan, ya yi kaurin suna a cikin sabuwar fin mai dogon zangon nan da ya yi fice mai suna "Labarina", inda ya fito a matsayin Excellency, mai neman takarar gwamna a makaranta, kuma babban aminin Lalle wacce ke kaunar Mahmud a cikin labarin. Amdaz na da sama da mabiya mutun dubu dari uku a instagram, kuma tini ya samu lambar sheda daga kwanfanin instagram da kan ta.

Leave your comment