Za A Kawo Karshen Gasar Da Rarara Ya Saka

Photo source : Instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin siyasa dan garin Kahutu dake jahar katsina, mazaunin jahar Kano Alhaji Dauda Kahutu Rarara, ya banyana cewa za a kawo karshen gasar rawa daya saka a kwanakin baya mai taken "Abamu Ahuta Dance competition", a ranar Lahadi mai zuwa wanda ya kama 23 ga watan Mayu shekarar 2021.

Fitaccen mai shirya fim a masana'antar Kannywood Bashir Mai Shadda ne ya sanar da hakan ta cikin wani fefen bidiyo da ya fitar a shafin sa na instagram jiya Alhamis da yanma, inda ya baiyana cewa Rarara ya tsirya kawo karshen wannan gasa ta rawa bisa taimakon alkalai da za su yi alkalanci akan wadan da su ne su ka samu nasara, sannan a gobe ranar lahadi duk za'a raba wa duk wadan da su ka yi nasara kyaututtukan su a katafaren hotel din Bristol palace dake jahar Kano.

Yk Designer Zai Saki Sabuwar Waka

Kyautukan da alkalan za su baiwa wadan da su ka samu damar lashe gasar suna da dama, wanda sun hadar da kudade, motoci, babura mai kafa uku da kuma mashina kirar roba roba. Tini bidiyon yan rawa daban daban ya ke cigaba da baiyana a kafafan sada zumunci na zamani, da su ka hadar da instagram, facebook da ma YouTube.

Jama'a dai sun zuba ido su ga su waye za su yi nasara a wannan gasar rewar da aka saka a madadin dan takarar shugabancin Jam'iyar APC ta kasa wato "Yari".

Nazifi Asnanic Ya Saki Sabuwar Waka

Leave your comment