Nazifi Asnanic Ya Saki Sabuwar Waka

Photo source : Instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawaki kuma mai bada shirya finafinai a masana'antar fim ta Kannywood Nazifi Asnanic ya saki sabuwar waka mai suna "Labari na", a cikin watan nan da muke ciki ta Mayu 2021.

Mawakin ya saki wakar "Labarina na" ne, dan bikin cika shekara goma da fara wakar Hausa na salon Nanaye, wanda matashin makadi Amude Booth ya yi aikin wannan sabuwar wakar. Kuma tini mawakin ya sanar wa masoyan sa fitowar wannan sabon aikin tare da sheda mu su cewa, wannan shekara goma daya yi yana waka, somuntabi ne, domin yanzu ne ma aka fara tafiyar kuma abun da aka sa gaba za'a cinma fiye da yadda ake gani.

NT4 Sun Saki Sabuwar Waka

Nazifi Asnanic na daga cikin manyan mawakan Nanaye da su ka shufa a wakokin soyayya da dama, musanman wadan da jaruman fim su ke hawa a cikin finafinai. Sannan a fanning wakokin siyasa ma, Nazifi Asnanic ya yi shura anan ma, musanman wakar sa ta senator Baraka da yayi wa tsohon gwamnan jahar Kano engineer Rabiu Musa Kwankwaso a shekarun baya lokacin da ya ke neman gwamnan Kano a karo na biyu. Kuma wakar ta yi tasiri matuka a nasarar tsohon gwamnan.

Mutun Dubu Goma Sha Bakwai (17,000) Sun Ga Bidiyon Hamisu Breaker A Ranar Farko.

Tini mawaka da dama su ka fara taya Asnanic murnar kai wa wannan shekaru a masana'antar tare fatan samun karin nasarori nan gaba.

Leave your comment