Mutun Dubu Goma Sha Bakwai (17,000) Sun Ga Bidiyon Hamisu Breaker A Ranar Farko.

Photo source : Youtube account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa na salon Nanaye daga masana'antar Kannywood wato Hamisu Breaker,  ya saki sabuwar fefen bidiyon wakar sa mai taken "Sai da ke", a jiya Laraba 19 ga watan Mayu 2021, kuma tini sama da mutun dubu goma sha bakwai su ka kalla a cikin kwana daya da fitar bidiyon, wacce a kwanakin bayan nan ne audio din wakar ta fita a kafafan sadarwa mabanbanta na zamani.

Manajan mawakin ne wato makadi "Kasheepu", ya sanar da hakan a shafin sa na instagram a yanmacin yau Alhamis 20 ga watan Mayu ta 2021. Inda ya sanar cewa wakar na ta goma sha takwas (18), a cikin jerin wakokin ta ke tashe a YouTube a yanzu haka, kuma har sama da mutane dubu goma sha bakwai sun ga wannan bidiyo ta "Sai da ke", a cikin kankanin lokaci.

Deezell Zai Fitar Da Waka Mai Mawaka 22 A Ciki

Ana sa ran idan wannan adadin ya cigaba a haka, to nan da wata daya wannan bidiyo zai iya samun yan kallo da su ka kai mutun dubu dari biyar zuwa miliyan daya. Wanda Hamisu Breaker ya juma da fara tara yan kallon da su ka kai wannan adadin a wasu wakokin da ya saki a baya.

Bidiyon dai, wanda kwarenren daracta wanda ya bada umarnin wakar mawaki Namenj da Hamisu Breaker mai taken "Dama" ya yi aikin, ya fita daban da dukkan nin aiyukan da mawaki Breaker ya taba fitarwa a fanin kwarewar aiki da tsarin labari, kamar yadda wasu masana wakokin Hausa na zamani da su ka kalli wannan bidiyo su ka sheda wa majiyar mu ta Madubi Naija bayan da su ka kalli bidiyon.

Dj Cinch Ya Samu Shedar Kammala Wani Taro Daga Kasar Amurika

Leave your comment