Dj Cinch Ya Samu Shedar Kammala Wani Taro Daga Kasar Amurika

Photo source : Instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen matashin mawakin Hausa na salon Hip Hop mazauni kuma dan asalin jahar Kaduna dake Arewacin Najeriya "Dj Cinch", wanda a cikin makonnin daya ya sanar cewa zai saki sabuwar waka mai taken "Credit alert", ya samu lambar yabo ta kammala wani taron atisayi akan waka daga kasar Amurika.

Deezell Zai Fitar Da Waka Mai Mawaka 22 A Ciki

Mawaki Dj Cinch ya sanar da hakan ne a shafin sa na instagram, inda ya sheda wa masoyan sa da cewa wannan lambar yabo da ya samu babban nasara ce ga wakar da yake yi kuma hakan zai kara daga matsayin sa, musanman idan aka yi la la'akari da darajar kasar Amurika da su ka shirya taron koyar da raira waka da gudanar da wasa a gaban yan kallo.

Deezell ya Kafa Tarihi a Hausa Hip Hop

Tin bayan cin gasar waka da fitaccen makadi Chopsticks da gidan radio ta sound city su ka sa, Dj Cinch ya kara bungasa damar sa wajan fitar da aiyuka daban daban a cikin yan shekarun da mawakin ya samu wannan nasarar, yanzu haka Dj Cinch ya sanar da ranar Asabar da safe ne wakar sa sabuwa ta credit alert zata fito ga mutanan gari su saurara.

Leave your comment