Deezell Zai Fitar Da Waka Mai Mawaka 22 A Ciki

Photo source : Instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop mazaunin kasar Amurika dan asalin jahar Kano wato Ibrahim Ahmad Rufai, wanda aka fi sani da suna "Deezell", wanda a kwanan nan ya dawo Nigeria daga kasar ta Amurika dan gudanar da bikin sallah karama, ya sanar da zai fitar da waka mai dogon zango dake dauke da mawaka mutun 22.

Deezell ya Kafa Tarihi a Hausa Hip Hop

Deezell ya baiyana hakan ne ta shafin sa na instagram, bayan da ya wallafa hotunan wakar tare da sheda cewa zai fitar da audio da bidiyo din wakar idan mabiyan sa su ka maida mai martani dubu uku.

Kusan wannan shine karo na uku ko hudu da mawaki Deezell ke hado kan mawaka daga jahohin Arewa, dan su yi waka tare, kuma mawaka manya da kanana daga ko wani jaha. Domin ya tallafa wa mawaka kanana masu tasowa daga bangarori daban daban. 

Dabo Daprof Nna Shirin Tagwayen Bbikin Zagayowar Ranar Haihuwar Sa Da Kuma Na Cika Shekaru Goma Sha Daya Da Fara Waka

Ana sa ran a yan kwanakin nan ne Deezell zai fara sakin wakokin masu dogon zango a shafin sa na YouTube.

Leave your comment