Dabo Daprof Nna Shirin Tagwayen Bbikin Zagayowar Ranar Haihuwar Sa Da Kuma Na Cika Shekaru Goma Sha Daya Da Fara Waka

Photo source : Instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin Hausa Hip Hop, marubuci, mai gabatarwa a radio kuma daya daga cikin mawakan da jahar Kano ke alfahari da su a masana'antar Hausa Hip wato "Dabo Daprof", wanda duniya ta sani da Mister Ladagoma, na shirin bikin zagayowar ranar haihuwar sa da kuma bikin cika shekara goma sha daya da fara waka a masana'antar Hausa Hip Hop.

Manajan mawaki Dabo Daprof da ake kira Icon Farouk ne ya baiyana hakan a wani dan karo da makusantan mawakin su ka shirya dan tattauna akan batun tagwayen bikin da zai gudana a farkon wata mai kamawa.

Mawakan Kano Sun Yi Shirin Sallah A Gidan Radio Freedom

Wannan shine taro na farko da mawaki Dabo Daprof zai hada dan bikin zagayowar ranar haihuwa ko na cikar shekaru da fara waka. Ana sa ran za a gudanar da taron ne iya makusantan mawakin na dangi, abokai da masoya na kusa. Kuma akwai shirye shirye da dama da za su gudana a wajan taron da su ka hadar da wake wake, jawabi daga bakin mutane da dama da dai sauran su.

Wannan ne karo na farko da wani mawakin Hausa Hip Hop daga Kano zai yi makamanciyar wannan 3rd taron, kuma ana ganin zai zama abun koyi ga sauran mawakan da ke wannan masana'antar ta Hausa Hip Hop.

"I Will Tell My True Story Myself" - Sound Sultan on Throat Cancer Reports

Leave your comment