Mawakan Kano Sun Yi Shirin Sallah A Gidan Radio Freedom

Photo source : Instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Wasu fitattun mawaka yan jahar Kano manya da masu tasoywan cikin su, sun yi shirin sallah na musanman a gidan radio Freedom dake jahar Kano a yau alhamis 13 ga watan Mayu 2021, wacce ita ce ranar sallah karama ta bana bayan da aka yi azumi talatin a bana sakamakon rashin tabbacin ganin watan shauwal.

Taro wanda gidan radio Freedom ta gabatar a karkashin jagorancin Abubakar Musa Labaran, a bisa tallafin mawaki Dabo Daprof, ya samu halattar mawakan Hausa na salon Nanaye mutun uku, da su hakar da matashin mawaki mai suna Abba dalibin waka. Sai fitaccen mawaki Ahmad Delta sai kuma shahararren mawaki Nura M. Inuwa da shima ya halaccin shirin.

Babayanks, Mr 442 Da Madox Za Su Saki Sabuwar Wakar

A bangaran mawakan zamani na Hausa Hip Hop kuwa, suma sun samu wakilcin mawaka mutun uku, da su ka hadar da fitaccen matashin mawaki Fresh Emir(Aku mai bakin magana), sai shima sanannan mawaki YK Designer da kuma mawakiya mai tasowa wato Jamcy.

An fara wannan shiri na musanman ne da karfe 12:30 zuwa karfe 2:00, inda mawakan su shida aka fara da saka wakokin su, sannan gabatarwa ya biyo baya sannan a karshe fitaccen matashin mai buga jita "David Swuazo" ya buka wa mawakan kida da Jita su kuma su ka raira waka a kai.

Mawaki 442 Ya Baiya Bakin Cikin Sa Da Dokan Lock Down Karo Na Biyu

Leave your comment