Babayanks, Mr 442 Da Madox Za Su Saki Sabuwar Wakar

Photo credit: YK Designer instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitattun matasan mawaka yan asalin garin Zaria dake jahar Kaduna Babayanks Manjago tare da Mr 442 da kuma Madox tbb daga jahar Kano za su saki sabuwar wakar su mai taken "Cikin mutunci" a yau 12 ga watan Mayu 2021.

Mawaki 442 ya baiyana hakan ne a shafin sa na instagram tare da sanar wa masoyan sa cewa wannan wakar zai fito a shafin YouTube da sauran duk wani shafin sauke waka cikin sauki, kuma ya na kira da su je su saurara.

Dj Cinch Zai Saki Sabuwar Waka

Mr 442 wanda a watannin da su ka shige ne na karshen watan Maris su ka fitar da wakar "Sai Monday" tare da mawaki Madox dan asalin jihar Kano, wanda su ka yi fada da shi a kwanakin baya kafin daga bisani su shirya tsakanin su. Haka zalika Babayanks, Mr 442 da Madox tbb duk sun fito a wakar Deezell mai taken "Duk abun da zai faru ya faru" tare wasu mawakan mutun goma sha shida da Deezell ya saka a cikin wakar.

Daga nan Mdundo mu na cigaba da bibiyar mawakan, dan sanin wani abu sabo za su fita dan mu sanar wa mabiyan mu.

Jaruma Tima Yola Ta Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Ta.

Leave your comment