Jaruma Tima Yola Ta Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Ta.

Photo source : AleeGee instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitacceyar matashiyar jaruma a masana'antar shirya finafinai ta Kannywood wato jaruma "Tima yola", wato Rukayya a cikin fitaccen shirin "Labarina", ta yi bikin zagayowar ranar haihuwar ta a yau Talata 11 ga watan Mayu 2021.

Chizo Germany Ya Saki Sunayan Wakokin Da Ke Cikin Sabuwar Kundin Sa

Da sanyin safiyar yau ne jarumar ta sanar da hakan, bayan da ta wallafa wasu hotunan ta a shafin ta na instagram, inda jarumar ta gode wa Allah da ya raya ta tsawon wadan nan shekarun kuma ta kasance cikin koshin lafiya. Sannan ta nemi masoyan ta da su taya ta murnan ganin wannan ranar.

Jaruma Tima yola, wacce ta ke cikin jerin jarumai mata ma su mabiya a halin yanzu, musanman a shafin instagram, ta fito a finafinai da dama wadan da su ka yi tashi.

Kuma jarumar na cigaba da taka rawar gani a cikin masana'antar ta Kannywood. Fim din "Labarina", na daya daga cikin fim din da ya kara fito da jaruma Tima yola a idon ma'abota kallon finafinan Kannywood, duba da irin rawar da jarumar ta taka a cikin wannan fim din da ta fito a matsayin kawar jaruma Nafisa Abdullahi wato "Sumaiya".

Mawaki 442 Ya Baiya Bakin Cikin Sa Da Dokan Lock Down Karo Na Biyu

Leave your comment