Mawaki 442 Ya Baiya Bakin Cikin Sa Da Dokan Lock Down Karo Na Biyu

Picture source: Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren matashin mawakin Hausa Hip Hop dan asalin garin Zaria dake a jahar kaduna Mr 442, ya nuna rashin jin dadin sa akan dokar kunle (lock down) da gwamnati ta sanya a daren yau Talata a dukkannin jahohin Najeriya gaba daya. Wannan dokar bayi wa mawakin dadi ba ko kadan.

Dj Ab Na Shirin Sakin Sabuwar Fefen Bidiyo

Mr 442 ya sanar da hakan ne ta cikin wani fefen bidiyo da ya wallafa na wani jamiyin gwamnati a tashar talabijan na kasa ta NTA, inda ya ke baiyana wa jama'a cewa, sakamakon bulluwar cutar Corona virus (Covid 19) a mataki na hudu, ya sanya gwamnati daukan wannan hukunci a cikin gaggawa domin tsare rayukan Al'umma.

Dokar wanda zai hana zirgazirgan mutane da ababan hawa daban daban, kuma kananan ma'aikata ma za su zauna a gida daga matakin aiki na 12, sai wajanjan taro na bukukkuwa za su rufe, haka zalika wajan saida abinci za su fara yin take away maimakon a ci a wajan.

Chizo Germany Ya Saki Sunayan Wakokin Da Ke Cikin Sabuwar Kundin Sa

Mr 442 wanda na daya daga cikin mawakan da su ke da wasanni da sallah a jahaho daban daban ya koka ganin yadda tini ya sanar da zuwa wadan nan garurruwan ga masoyan sa a kwanakin baya bayan nan.

Leave your comment