Dj Ab Na Shirin Sakin Sabuwar Fefen Bidiyo

Picture source: Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jahar Kaduna kuma daya daga cikin mawakan da ke lokaci a masana'antar ta Hausa Hip Hop wato "Dj Ab " ya na shirin sakin sabuwar fefen bidiyo a cikin yan kwanaki ma su zuwa, duk da babu wani gamsasshiyar bayani da ke baiyana sunan wakar ko lokacin fitowar ta na hakika.

M-kay Ya Taya Mahaifiyar Sa Murnar Ranar Uwa Ta Duniya.

Mawaki Dj Ab a yan kwanakin nan, ta shafukan sa na sada zumunta daban daban, ya na ta wallafa hotuna da ya dauka na bayan fage, a lokacin da ake daukan wannan sabon aikin bidiyo, tare da sheda wa mabiyan sa cewa wani abu babba na nan tafe a dan lokaci kalilan.

Dj Ab kamar yadda aka sani tin a shekarun baya, ya ke baiwa masoyan sa nishadi babu kama hannun yaro a fanni daban daban, musanman tun lokacin da Dj Ab ya fara wakoki shi kadai ba tare da ta hada ka da ya saba tare da yan Y.N.S ba.

M-kay Ya Taya Mahaifiyar Sa Murnar Ranar Uwa Ta Duniya.

Ko a kwanakin baya, Dj Ab ya sanar da cewa ya yi waka tare da shahararren mawakin Afro Pop "Mr Eazy", wanda ya ke baiwa Dj Ab gudunmawa wajan daukan nauyin yiwa Dj Ab bidiyo ta wakar sa mai taken "Kumatu" Kuma ya baiyana cewa zai sake daukan nauyin wani bidiyon.

Leave your comment