Dj Cinch Zai Saki Sabuwar Waka

Picture source : Dj Cinch instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen matashin mawakin Hausa na salon Hip Hop mazauni kuma dan asalin jahar Kaduna dake Arewacin Najeriya "Dj Cinch", zai saki sabuwar waka mai taken "Credit alert" a cikin yan kwanaki ma su zuwa.

Mawaki Dj Cinch ya sanar da hakan ne a shafin sa na instagram, inda ya sheda wa masoyan sa da cewa wannan waka zai fito nan ba da jumawa ba, kuma za su iya sauke ta a wayoyin su ta manhajoji daban daban idan lokacin ya yi.

Jaruma Tima Yola Ta Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Ta.

Dj Cinch wanda a kwanakin baya ya fitar da sabuwar waka mai taken "Cigaba da gashi", ya na daya daga cikin matasan mawakan da ake ji da su a masana'antar Hausa Hip Hop, ake kuma sa ran za su shiga sahun mawaka irin su Dj Ab da dai sauran su wadan da a halin yanzu da su ta ke yi kuma su na da tarin masoya a Arewacin kasan nan da ma sauran sassa a duniya kuma yan Kaduna ne.

"Credit alert", waka ce akan kudi da bukatuwa ga samun su, wanda a halin yanzu su ne kan gaba wajan neman biyan bukatar yau da gobe.

Mawaki 442 Ya Baiya Bakin Cikin Sa Da Dokan Lock Down Karo Na Biyu

Leave your comment