Deezell ya Kafa Tarihi a Hausa Hip Hop
24 May 2021
Photo source : Instagram account
By Omar Ayuba Isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop mazaunin kasar Amurika dan asalin jahar Kano wato "Deezell", ya kafa tarihi a masana'antar Hausa Hip Hop, inda ya zama mawaki na farko a tarihin mawakan Hausa Hip Hop daya fi ko wani mawaki mabiya a shafin instagram a cikin shekarar 2021.
Shafin Madubi Naija ne ta baiyana wannan labarin, bayan da ta gudanar da bincike akan mawakan Hausa Hip Hop masu tarin mabiya a shafin instagram a yau laraba 19 ga watan Mayu 2021.
Deezell Ya Dawo Nigeria Bikin Sallah.
Inda binciken ya nuna cewa mawaki Deezell ne akan gaba wajan tarin mabiya a instagram, inda mawakin ke da mabiya akalla mutun dubu dari tara da dubu ashirin da hudu, (924,000). Wanda yanzu hakan ya sa ya dara Dj Ab wanda shi ke jan ragamar kafin yanzu.
Deezell, wanda zai saki wata waka daya hada manyan mawakan Hausa Hip Hop dama kanana mutun ashirin da biyu (22), bayan da ya saki wakar "Duk abun da zai faru ya faru" mai mawaka goma sha shida (16), yana kan gaba a shafin twitter nan ma inda tini ya samu shedar ingancin account din sa na instagram da na twitter din.
Feezy Ya Saki Sabuwar Waka Ta Sallah Tare Da Yan Uwan Sa Biyu.
Leave your comment