Deezell Ya Dawo Nigeria Bikin Sallah.

Photo source : Instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop mazaunin kasar Amurika dan asalin jahar Kano wato "Deezell", ya dawo Nigeria daga kasar ta Amurika dan gudanar da bikin sallah karama da aka gudanar a yau Alhamis 13 ga watan Mayu ta 2021.

Deezell ya baiyana dawowar sa ne ta shafin sa na instagram, bayan da ya wallafa hotunan sa tare da matar sa "Jiddah" da kuma wani hotun tare da manajan sa "Cdeeq", sanye da manyan kaya dake nuni da bikin sallah su ke.

Kusan wannan shine karo na uku ko hudu da nawaki Deezell ke dawowa daga kasar Amurika zuwa Nigeria kasar sa ta haihuwa duk a shekarar 2021. Inda kwanaki ya shigo aikin wata wakar hadaka tare da mawaka da dama, ya kuma shigo kafin nan inda ya zo wa matar sa ziyarar bazata.

Mawakan Kano Sun Yi Shirin Sallah A Gidan Radio Freedom

Ana sa ran a yan kwanakin nan ne Deezell zai saki wata waka daya hada manyan mawakan Hausa Hip Hop dama kanana bayan da ya saki wakar "Duk abun da zai faru ya faru".

Feezy Ya Saki Sabuwar Waka Ta Sallah Tare Da Yan Uwan Sa Biyu.

Leave your comment