Yk Designer Zai Saki Sabuwar Waka

Photo source : Instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen Matashin mawakin Hausa Hip Hop, R and B da kuma Afro pop dan jahar Kano mai suna Yusuf Muhammad, wanda ake wa lakabi da suna "YK Designer" zai saki sabuwar waka mai taken "Kina ina" a cikin yan kwanaki ma su zuwa.

Mawakin ya baiyana hakan ne ta shafukan sa na sada zumunci a yau Alhamis 20 ga watan Mayu ta shekarar 2021, a cikin wani sanarwa da ya fitar karkashin hoton wannan sabuwar waka da mawakin ya wallafa.

Nazifi Asnanic Ya Saki Sabuwar Waka

YK Designer yana wannan sanarwar ne jin kadan bayan da gidan talabijan ta Arewa24 su ka sanar da cewa za su harka hirar mawakin tare da mai gabatarwa Nomiss Gee a daran Alhamis din, wanda wannan shine karo na farko da mawaki YK Designer zai yi hira a tashar, tin bayan fara saka wakar sa a a cikin shirin Zafafa Goma da Nomiss Gee ke ganatarwa a tashar Arewa24 din.

Kina ina wakar Soyayya ce mai dauke da labari mai ban tausayi, ban haushi da kuma nishadi tare da rikitarwa, YK ya yi wakar ne tare da matashin mawaka kuma makada biyu, wato Amude Booth wanda shi ya yi kidan, sai kuma DM wanda shi ya daukin nadi muryar tare da gyara ta.

NT4 Sun Saki Sabuwar Waka

Ana sa ran mawaki YK Designer zai fitar da kundin wakoki a cikin shekarar nan ta 2021, bayan da cutar Covid19 ya hana hakan faruwa a shekarar data gabata. A cewar manajan mawaki YK Designer wato fitaccen mawakin Hausa Hip Hop Dabo Daprof (Mister Ladagoma).

Mutun Dubu Goma Sha Bakwai (17,000) Sun Ga Bidiyon Hamisu Breaker A Ranar Farko.

Leave your comment