Sals Fateetee sun yi waka tare da Pheno B dan kasar Nijar

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitacciyar mawakir Hausa mai salon R and B yar garin Abuja Sals Fateetee tare da babban mawakin Hausa Hip Hop dan kasar Nijar Pheno B sun saki sabuwar waka mai taken "Ke ni ke so" a yau laraba 9 ga watan Uni ta 2021.

Fresh Emi ya hadu da mataimakin gwanman Kano

Sals Fateetee ta sanar da hakan ne a shafin ta na instagram, inda mawakiyar ta sheda wa mabiyan ta cewa wannan waka da su ka yi tare da mawaki Pheno B tini ta fita a ko ina kuma yanzu haka za a iya saurara daga ko ina ina aka sauke wakar wanda ke kan manhajojin sauke wakoki daban daban na duniya.

Wannan wakar mai taken "Ke na ke so", shi ne waka ta farko da mawakan biyu za su tare tin bayan haduwar su a kasar ta Nijar, inda Sals Fateetee ta je gudanar da wani wasa a bikin al'ada da su ke gudanarwa a kasar.

Za A Kawo Karshen Gasar Da Rarara Ya Saka

Sals Fateetee na daya daga cikin manyan matan Arewa da ke tashe a halin yanzu, kuma salon ta ya fita daban da na sauran mata masu waka, duba da irin aikin da take samu tin daga kan audio har ma ga bidiyo.

Leave your comment