Fresh Emir ya hadu da mataimakin gwanman Kano

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jahar Kano kuma daya daga cikin matasan mawakan da ake yayi a halin yanzu "Adam Abdullahi", wanda aka fi sani da "Fresh Emir" (Aku mai bakin magana), ya kai wa maitaimakin gwamnan jahar Kano "Dr Nasiru Sule Gawuna" ziyarar ban girma a cikin makon nan da mu ke ciki.

Ado Gwanja ya saki bidiyon wakar "Naji dadi"

Fresh Emir ne ya sanar da hakan a cikin hoton sa da mataimakin gwamnan a offishin sa, bayan da su ka hadu a wajan wani taro a jamiyar Bayero da ke Kano a watanni da su ka wuce, kuma ya burge mai girma mataimakin gwamnan bayan da ya gudanar da wakokin fadakarwa da aka san shi da su a gaban Dr Gawunan, kuma mataimakin ya bukaci a kawo mai Fresh Emir su gaisa hannu da hannu, ya kuma yaba ma sa bisa kokarin da ya ke, musanman irin wakokin da ya ke.

Za A Kawo Karshen Gasar Da Rarara Ya Saka

Duk da ba a san mai wannan alakar za ta haifar ba na tsakanin mawakin da mataimakin gwamna, amma ana ganin dama ce ga Fresh Emir da ya shigar da kudirin abubuwan da ke damun matasa da kuma mean ya za a samar mu su da mafita a cikin wannan gwamnatin mai ci yanzu.

Leave your comment