Ado Gwanja ya saki bidiyon wakar "Naji dadi"

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa na salon Nanaye kuma babban jarumi a masana'antar fim ta Kannywood "Ado Gwanja" ya saki bidiyon sabuwar wakar sa mai taken "Naji dadi" kamar yadda mawakin ya yi alkawari.

Za A Kawo Karshen Gasar Da Rarara Ya Saka

Ado Gwanja ne ya sanar da fitowar wannan wakar a shafin sa na instagram bayan da ya wallafa kadan daga cikin bidiyon a shafin na sa, kuma ya sheda wa masoyan sa cewa tini wannan wakar ta riga ta fito a shafin YouTube din sa ga ma su sha'awar kallon bidiyon sai su garzaya shafin na sa na YouTube.

Kasheepu da mawaki Ahmad Delta sun saki sabuwar waka

Tini manya da kananun mawaka da jaruman Kannywood su ka fara daura wannan wakar a shafukan su dan mara wa Ado Gwanja baya kamar yadda su ke wa junan su yanzu.

Ado Gwanja ya yi aikin wannan bidiyon ne a jahar Kaduna, tare da mata da yan rawa da dama, kuma mai bada umarnin bidiyon wakokin Umar MB ne ya yi aikin wannan bidiyon.

Leave your comment