Kasheepu da mawaki Ahmad Delta sun saki sabuwar waka
10 June 2021
By Omar Ayuba Isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Fitaccen mawakin Hausa na salon Nanaye kuma babban makadin da ake yayi yanzu dan jahar Kano, kuma daya daga cikin manyan makadan Nanaye da ke kan gaba a wajan yi wa mawaka wakoki ma su tashe "Kasheepu" ya saki sabuwar waka tare da fitaccen mawakin Hausa Ahmad Delta.
Za A Kawo Karshen Gasar Da Rarara Ya Saka
Wakar mai taken "Daure", shi ne wakar makadi Kasheepu na biyu da zai fitar a cikin shekarar nan ta 2021 tare da babban mawaki daga bangaran mawakan Nanaye, tin bayan wacce su ka yi da mawaki Nura M. Inuwa mai taken "Mu gudu tare".
ya kuma sanar da hakan ne a shafin sa na instagram, inda ya daura bidiyo yana bin wakar a cikin studio, sannan ya tabbatar wa masoyan sa da cewa wannan wakar zai fito nan ba da jumawa ba.
Nazifi Asnanic Ya Saki Sabuwar Waka
Kasheepu wanda shi ne makadi kuma manajan fitaccen mawaki Hamisu Breaker, ya yi mawaka irin su Ali Jita, Ado Gwanja, Umar M. Shareefy, Ahmad Delta, Fresh Emir, Amdaz da dai sauran su aiki daban daban, kuma ana ganin salon kidan sa daban ya ke da na sauran makadan zamani dake kida a arewacin Najeriya.
Leave your comment