Mawaki 442 ya zaki sabuwar waka

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop daga Zaria dake jahar Kaduna, Mr 442 ya fitar da sabuwar waka tare da Zannu da kuma fitaccen mawaki Teeswag mai taken "Rayuwa".

Sals Fateetee sun yi waka tare da Pheno B dan kasar Nijar

Mawakin ya sheda wa masoyan sa hakan ne ta shafin sa na instagram, ta cikin wani hoto mai dauke da murya da ya daura yau da rana, yayin da ya tabbatar da fitowar wannan waka da su uku su ka yi a manhajojin daban daban na sauke a
Wakoki.

Fresh Emi ya hadu da mataimakin gwanman Kano

Mr 442, wanda ahalin yanzu ke garin Lagos inda ya je hutawa tare da wa su aiyukan, yana daga cikin mawakan da su ke sakin sabbin wakoki akai akai a yan kwanakin nan, kuma ko a cikin watan nan da mu kai bankwana da shi, ya saki wakar da ya yi mai taken "Sai me nene". Kuma ana cikin yayin ta ne ya kara sakin wakar, duk da hakan wani lokacin kan zama cigaba ga mawaki sakin waka akai akai, a wasu lokutan kuma matsala take haifar wa. Za mu yi rahoto na musanman game da ra'ayin mutane akan wannan batun.

Leave your comment