An nada Sojaboy a mazaunin Yarima

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararen jarumin 90 days fiance da kuma mawaki, Usman Umar wanda aka fi sanin sa da lakabin SOJABOY ya samu karin daukaka a rayuwarsa. 

A daren jiya ne ya bayyana a kan shafin sa na sada zumunci (Instagram) cewa an nada shi sarauta da mukamin Yariman Gidan Igwai. 

Hamisu Breaker zai saki kundin fefen sa ranar Yuli 21

Ya rubuta kaman haka "Barkan kudai iyalai na da abokan arziki. Ina farin cikin sanar da ku cewa an bani mukamin Yariman Gidan Igwai kuma ina gayyatar ku baki daya." 

Nadin dai za ayi shi ne ranar 24 ga watan Yuli, 2021 a jihar Sakwato, Najeriya.

Fitattun record labels 5 dake kasar Najeriya

SOJABOY a halin yanzu ya saki kundin fefen wakar sa mai taken King Africa. Soja Boy ya samu daukakar sa ne a lokacin da ya fito a wani shiri mai dogon zango, shirin 90 days fiance yayin da ya auri wata ba'amurkiya mai sunan Lisa. Daga bisani sun rabu bayan rashin fahimtar da suka samu a tsakanin su. 

Da fatan Allah ya taya riko da jagora. 

Leave your comment