Fitattun Wakokin Arewa Guda 7 Agusta 2021

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

A cikin watan Agusta mawakan Arewacin Najeriya sun saki wakoki da dama face daga audio zuwa bidiyoyi. Bayan karin ingancin da aka samu wurin sarrafa ire-iren salon wakokin daga makada kwararru, masu bada umarni suma sun nuna bajintar su wurin inganta nasu ayukan. A halin yanzu dai, mawaka sun kara daura dammaran su wajen ganin ayukan su sun fito da inganci saboda masu kallo su nishadantu. Ga dai wakoki guda 7 wadanda suka yi shura a cikin watan na Agusta. 

7. Kaunar Ki - ZSquare Gombe 

Zsquare Gombe mawakin salon Afropop ne wanda ya kware a fannin wakoki irin na soyayya. Kaunar Ki waka ce ta soyayya wanda Malo Boi ya ba da umarni. HMK Shaba shi ya tace hoton aikin. 

6. Lukuti - DJ AB

DJ AB mawakin salon rap da Afropop ne wanda yake karkashin YNS. A halin yanzu dai, akwai kyakyawar alaka tsakanin shi da Empawa wanda hakan ne yasa ya saki wakar Lukuti karkashin su. Lujuti waka ce ta nishadi wanda sakon ke magana ne a kan halitar dan Adam a mazaunin koshashe. Feeiziey wanda yake karkashin YNS ne ya bada umarni. 

5. Mutumina - LsVee 

LsVee wanda yake kiran kan sa da lakabin Mamas Boy matashin mawaki ne wanda ke salon rap. Bidiyon mutumina yana magana ne a kan alakar da ke tsakanin mutane biyu. Larabeey filmworks ne suka bada umarnin wannan aikin.

4. Who be dis Guy - Kheengz tare da Falz & MI

Kheengz ko kuwa a ce YFK data ne daga cikin jagororin salon rap a Arewacin Najeriya da ma kasar baki daya wanda yake kokartawa wurin sakar ayuka masu inganci. A wannan karon dai ya hada gwuiwa ne da fittatin mawaka Falz da M.I wurin fitowa da wannan aikin mai taken Eho be dis guy, ma'ana "wanene wannan gayen". An aiwatar da aikin ne a birnin Iko dake can Lagos. Bash em shine wanda ya bada umarnin bidiyon aikin sannan  King Abdul shi ya dauki nauyin aikin. Music Nerd shi ya sarrafa wakar sannan Khaymix ne ya kula da na'urar tace wakar. 

3. Cikin Mutunci - Baba Yanks da Madox TBB da Mr 442

BabaYanks Manjago daya ne daga cikin mawaka masu tasowa wanda ya gayyaci Madox da Mr 442 cikin wannan aikin. Matasan sunyi kokari sosai dyba da irin salon da aka dauki aikin. Cikin mutunci waka ce mai cike da nishadi sannan S.O.S Expressions sun yi matukar kokari wajen bada umarni.

2. Mulki - Morell

Musa Akila wanda aka fi sani da Morell daya ne daga cikin jagororin salon hiphop musamman a Arewacin Najeriya. Mulki waka ce dake kunshe cikin sabon fefen da ya saka mai taken MANSA. An aiwatar da aikin ne a jihar Abuja. Spotlyt shi ne wanda ya bada umarni wurin sarrafa bidiyon aikin. 

1. Anzo Wurin - Nomiis Gee da Ricqy Ultra 

Anzo Wurin daya ne daga cikin ayukan da mawakan biyu wato Nomiis Gee da Ricqy Ultra suka saka bayan Kuna Ina. Anzo wurin waka ce da ta zo da salon Afropop wanda za a iya cewa waka ce ta nishadi. Anyi matukar kokari daga yanda aka tsara dandalin, fuskokin da aka gayyata da ingancin aikin. A cewar mawakan biyu, an kashi fiye da naira miliyan daya da rabi wurin aiwatar da aikin.  KefaZz Simple Touch ne ya sarrafa kidan wakar karkashin QRY MUSIQ. Rabs Mada shi ya jera kuma ya tace hoton aikin hade da Sandros. Muhsin Bako da KG Designs sune suka dauki hoton aikin. KaiKauce Class sune suka dau nauyin aikin da bada umarni. 

Leave your comment