Anyi kira ga Hamisu Breaker da ya fara fassara bidiyon wakokin sa zuwa turanci dan masu jin sa daga wasu kasashen

Image source: Hamisu Breaker Instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Wasu daga cikin masoyan fitaccen mawakin zamani na salon Nanaye wanda ake yayi "Hamisu Breaker Dorayi", sun yi kira ga ga mawakin, da ya fara fassara bidiyon wakokin sa zuwa turanci dan masu jin sa daga wasu kasashen musanman wadan da ba hausawa ba ne kuma ba sa jin mai yake fada.

Za A Kawo Karshen Gasar Da Rarara Ya Saka

An yi wannan kiran ne ga Hamisu Breaker a cikin yan kwanakin nan tin bayan da ya saki sabuwar fefen bidiyon wakar "Sai da ke", wanda ake ganin wannan Bisayo ya kafa tarihin da babu wani bidiyon Mawakin Hausa na salon Nanaye da samu kwarenren aiki irin wannan bidiyo a cikin shekarar 2021.

Da dama daga cikin wadan da su ka kalli wannan bidiyon, sun yi kira ne ga mawakin da ya d
Fara hada wa da fassarar wakar a cikin bidiyon sa da ya ke saki, dan kara samun shiga da karbuwa a gurin mutanan da salon Hamisu Breaker ta ke burge su amma ba hausawa ba ne ko kuma basan jin mai yake fada a cikin wakar.

Nazifi Asnanic Ya Saki Sabuwar Waka

A cikin mawakan da su ke wannan salon fassara wakar su izuwa harshen turanci a cikin fefen bidiyon su, sun hada da Diamond platinumz, Lavalava, Mbosso, Reyvanny da Harmonize duk kan su yan kasar Tanzania, anan ma Arewa, Akwai mawaki Hausa Hip Hop "Fresh Emir " (Aku mai bakin magana), wanda ya ke da kokarin Fassara bidiyon wakokin za izuwa yaren turanci, wanda babban mawaki kuma marubuci "Dabo Daprof" ne ke fassara wadan nan wakokin na "Fresh Emir".

Ana fatan dai mawaki Hamisu Breaker da masu gudanarwar sa za su dauki wannan shawarar su kuma fara fassara wakokin sa a bidiyon da ya ke fitarwa.

Leave your comment