Taaziyar Jaruma Daso Ga Sarkin Kano.

Picture source : Saratu Gidado instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Tsohuwar jarumar fim a masana'antar fim na Kannywood Hajiya Saratu Gidado wacce aka fi sani da suna Daso ta mi ka sakon ta'aziya ga sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, bisa rasuwar mahaifiyar sa wato mai babban daki Hajiya Maryam Ado Bayero, wacce ta rasu a wani asibiti a kasar misira a makon nan da ku ke ciki.

Anyi kuma jana'izar marigayiyan ne a ranar Litinin 26 ga watan Afrilu 2021. Bayan da aka dawo da gawar daga chan kasar ta misira. Dubunnan mutane ne su ka halacci jana'izar marigayiyar.

Taaziyar Jaruma Daso Ga Sarkin Kano.

Acikin wadan da kuwa su ka nuna ta su alhinin wannan rashin sun hada da jaruma Daso, wacce ta baiyana alhinin ta tare da rakon Allah ya gafarta wa mai babban daki Hajiya Maryam Ado Bayero.


Daso ta ce marigayiya mace ce mai kirki, mai son mutane, mara kyamar mutun duk talaucin sa, sannan mai son taimako. Har ta bada labarin haduwar su a lokacin da ta je fada dan gaida marigayiya a falon ta, sai ta kira sunan ta Saratu tare da shi mata albarka.

Mansura Isah Ta Koya Wa Nakasassu 50 Aikin Hannu

Marigayiya ta rasu ta bar yan uwa yaya da dama, cikin yayan ta akwai Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Larabeey Ya Saki Sabuwar Waka

Leave your comment