Larabeey Ya Saki Sabuwar Waka

Picture source : Larabeey's instagram 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen Matashin Hausa Hip Hop dan asalin jihar Bauchi Larabeey ya saki sabuwar waka mai taken "Ramadan Freestyle" a tsakiyar watan azumin watan Ramadan na bana.

Mawakin ya baiyana hakan ne a shafin sa na instagram tare sauran safukan sa, cewa wannan waka tini ta riga ta fito kuma masoyan sa za su iya zuwa yana gizo su sauke ta tare kallon bidiyon a YouTube.

An Cigaba Da "A Yau" Series Na Fresh Emir

Larabeey wanda daya ne daga cikin sanannun mawakan da jahar Bauchi ke ji da su a fannin Hausa Hip Hop ya yi wakoki da dama a baya ciki har da wacce ya yi tare da Classiq mai taken "Antashi", ya kuma fito a cikin wakar hada ka da fitaccen mawaki Deezell ya yi a kwanakin baya.

Manyan Jaruman Kannywood Sun Fito A Wani Fim Da Za'a Haska Ranar Sallah Karama

Leave your comment