An Cigaba Da "A Yau" Series Na Fresh Emir

By Kosiso

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen matashin mawakin Hausa Hip Hop Adam Abdullahi dan asalin jahar Kano da duniya ta fi sani da "Fresh Emir " zai saki sabuwar waka daga cikin kundin wakokin fadakarwar da mawakin ke yi ma su suna "A Yau", series, kashi na biyu a zango na biyu tare da bidiyon ta.

Anyi wannan bidiyon ne jiya yau lahadi 25 ga watan afrilu 2020, Mawakin ya sanar da fitowar wannan sabuwar waka da bidiyon ta a shafin sa na instagram, nan ba da jumawa ba, kuma anyi bidiyon wannan karon da salo na daban da yadda aka saba ganin bidiyon "A Yau" din.

Hamisu Breaker Zai Saki Sabuwar Waka


Wannan wakar da Fresh Emir ya yi, ya yi ta ne akan matsala da illar zinace zinace da ta yawaita yanzu a tsakanin al'ummar mu na Arewa. Tare da jan hankali mutane ga barin wannan dabiya mara kyau, da addini,  al'ada da ma masana lafiya su ke hani da shi saboda illar hakan ta fuskas sabon ubangiji,  zubar da mutuncin kai da kuma jefa kai ga halaka ta kamuwa da cutittukan zamani iri iri.


An dauki bidiyon wakar a jahar Kano, inda mai bada umarni MSK ya yi aikin tare da taimakon shima mai bada umarni Mus'ab Dauda Sadauki da aka fi sani da Director Mus'ab. Fitaccen Mawaki kuma Marubuci "Abdallah Amdaz" ne ya yi fitowa ta musanman a cikin bidiyon. Sai shima fitaccen mawaki kuma marubuci Dabo Daprof da ya yi fassara wakar zuwa harshen Turanci, yayin da makadi Mega mix ya yi aikin audio din wakar.

Manyan Jaruman Kannywood Sun Fito A Wani Fim Da Za'a Haska Ranar Sallah Karama

Tini sama da mutane dubu goma sha biyar da doriya su ka kallin wannan fefen bidiyo a shafin mawaki Fresh Emir na instagram daga lokacin da ta fito.

Leave your comment