Hamisu Breaker Zai Saki Sabuwar Waka

Photo credit : from Hasheepu instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin Hausa na salon Nanaye a masana'antar Kannywood dan asalin jihar Kano "Hamisu Breaker Daurari" zai saki sabuwar waka mai taken "Sai da ke" a cikin watan azumin Ramadan ta bana.

Wakar za ta fito ne a ranar Lahadi, biyu ga sabuwar watar Mayu ta 2021, wacce ta yi daidai da ashirin ga watan Ramadan. Kamar yadda sanarwar ya gabata a ta shafin instagram na makadin sa kuma manajan sa wato "Kasheepu Ahmad Record".


Hamisu Breaker wanda a halin yanzu na kan gaba a cikin mawakan da ake yayin su a mawakan Hausa kuma wakar sa n"Jaruma" ta bashi shahara ta daban a cikin fitattun wakokin da ya yi, yanzu haka yana daga kan gaba a masu samun mabiya wajan kallon wakokin su a manhajar YouTube da sauran manhajoji na waka.


Hamisu Breaker ya saki wakoki irin su Kalmar so, Masoyi Majinyaci ne, da kuma na baya bayan nan wato Yadda kunne ya ji, wanda wasu ke wa wakar lakabi da Dafin so. 

Manyan Jaruman Kannywood Sun Fito A Wani Fim Da Za'a Haska Ranar Sallah Karama


Kamar sauran fitattun wakokin sa, wannan sabuwar wakar ta "Sai da ke", makadi Kasheepu ne ya yi aikin ta, wanda kuma masoya da dama sun nuna kaguwar su da fitor wannan sabuwar wakar soyayyar da Hamisu Breaker zai fitar a mako mai zuwa idan mai guda ya nufe mu da gani.

Za ku samu wannan wakar a nan Mdundo ta ma sauran wakokin Hamisu Breaker da na wasu fitattun mawakan Hausa da sassa daban daban a Najeriya da duniya gabaki daya.

Ahmad Delta Ya Saki Sabuwar Waka

Leave your comment