Ahmad Delta Ya Saki Sabuwar Waka

Photo source : Ahmad Delta's official instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa na salon Nanaye mazaunin Kano, haihuwar jahar Delta dake kudancin Najeriya "Ahmad Delta", ya saki sabuwar waka mai taken "Ruwan Zuwa" a jiya alhamis 22 ga watan Afrilu 2021.

Mawaki Ahmad ya sanar da hakan ne a shafin sa na instagram, inda ya sheda wa masoyan sa da cewa wannan waka ta fito kuma za su iya sauke ta a wayoyin su ta manhajoji daban daban.

Manajan Deezell Ya Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Sa.

Ahmad Delta wanda a kwanakin baya ya fitar da sabuwar bidiyo ta watar "Rashin Masoyi" na daya daga cikin matasan mawakan da ake ji da su a masana'antar Kannywood, ake kuma sa ran za su shiga sahun mawaka irin su Hamisu Breaker da Garzali Miko da dai sauran su wadan da a halin yanzu da su ta ke yi kuma su na da tarin masoya a Arewacin kasan nan da ma sauran sassa a duniya.

Manajan Deezell Ya Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Sa.
Ruwan Zuma, waka ce akan soyayya da halin da mai yin ta ke shiga a lokacin da ta juya mai baya. Wanda da wannan salon aka san mawaki Ahmad Delta a cikin mawakan Kannywood ma su tasowa.

Leave your comment