Manajan Deezell Ya Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Sa.

Photo credit : Deezell instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Daya daga cikin sanannun manajojin mawakan Hausa Hip Hop kuma tsohon dan rawa kuma mawaki, Cdeeq, wanda manajan shahararren mawakin Hausa Hip Hop mazaunin kasar Amurika Deezell, ya yi bikin zagayowar ranar haihuwa a yau Alhamis 26 ga watan Afrilu 2021.


Mawaki Deezell ne ya sheda hakan a shafin sa na instagram dazu da rana da misalin karfe 3, inda ya daura hoton sa tare da rubutu sakon gaisuwa, yabo, jinjina, da kuma tsokana ga manajan na sa. Ya kuma baiyana wa duniya irin gudunmawar da ya samu daga wajan Cdeeq din tin daga haduwar su izuwa yanzu.


A cikin wadan da su ka mika ta su sakon taya murna ga manajan Deezell su hadar da fitattun mawakan Hausa Hip Hop irin su Dj Ab daga jahar Kaduna, Dabo Daprof daga jahar Kano, Fezzy kani ga Dj Ab, Bosskid famous daga Kano, Ovizta daga Kaduna.

Cdeeq Amas, dai ya mayar da martani ga Deezell cikin raha da barkwanci akan wannan taya shi murna da yayi, ta hanyar tambayar sa cewa "shin fatan alheri da yabo yake mai ko kuma tona mai asiri yake ga jama'a".

Mawaki Queen Zeeshaq Ta Yi Rabon Kayan Abinci Ga Mabukata

Leave your comment