Mawaki Queen Zeeshaq Ta Yi Rabon Kayan Abinci Ga Mabukata

Picture source : Queen Zeeshaq official facebook page 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakiyar Hausa Hip Hop yar asalin jahar Kano, kuma fitacciyar matashiyar ma'aikaciyar radio a Kano Zainab Ishaq wacce aka fi sani da suna "Queen Zeeshaq " ta yi rabon kayan abinci ga mabukata da kuma marayu a yau Litinin 26 ga watan Afrilu 2021, wanda ya yi daidai da sha hudu ga watan Ramadan.

Rahama Sadau ta Kara Rabon Kayan Abinci ga Mabukata
Ta yi wannan rabon kayan abincin ne a karkashin gidauniyar ta mai suna "Gatan Marayu Foundation" da take tallafawa marayu da iyayen su da kuma mara sa karfi, musanman ta cikin shirin da ta ke gudanarwa a gidan radio vision fm dake Kano.

An Kwace wa Mawakiya Queen Zeeshaq Instagram Account
Queen Zeeshaq ta raba kayan abincin Ramadan ga mabukata, wanda su ka hadar da danyen Shinkafa, Taliya, Makaroni, Garin tuwo, Gero, Wake, Maggi da kuma Gishiri. ta kuma yi rabon ne ba tare da samun tallafin wasu ba musanman ga kungiyar ta na marayu.


Wanann shine karo na farko da Mace mawaki a masana'antar Hausa Hip Hop za ta bada tallafi ga mabukata a cikin watan azumin Ramadan. Wanda hakan ya janyo hankalin mutane da dama wajan yaba wa kokarin ta akan wannan rabo da ta yi.

Jaruma Hafsat Idris ta Siyi Sabon Mota.
Zainab Ishaq wato Queen Zeeshaq, ta baiyana wa majiyar mu cewa, marayu su na cikin wani hali na matsin rayuwa, kuma su na da bukatar taimakon al'umma dan su ma su ji dadi da kuma saukin rayuwa kamar kowa.

Leave your comment