Rahama Sadau ta Kara Rabon Kayan Abinci ga Mabukata

 

[Photo cred :Instagram - Rahama Sadau]

by Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram


Shahararriyar jarumar fim a masana'antar Kannywood da Nollywood yar jahar Kaduna wato "Rahama Sadau" ta bude sabon watan azami ne da rabon kayan abinci ga mabukata da dama a ranar daya ga watan Ramadan ta shekarar 1442, wacce ta yi daidai da 13 ga watan Afrilu 2021. A jahar ta na haihuwa wato Kaduna.

Also Read: Jaruma Daso ta shiga sahun jarumai ma su taimakon Ramadan.

Bayan wannan lokacin, Rahama Sadau ta gudanar da wani rabon har kananan buhun shinkafa kwana dari biyar (500), a karkashin gidauniyar nan mai suna "Ray of hope foundation Africa", tare da taimakon wasu daga makusantan ta wajan gudanar da wannan abun alheri.

Tin abaya, daman jarumar na daya daga cikin jarumai ma su tallafawa mara sa karfi da marayu a karkashin kungiyoyin sa kai da tallafi da su ke da su. Jarumai irin su Saratu Gidado, Hadiza Gabon, Hafsat Idris da matar Sani Danja Mansura Isah, na kan gaba a jarumai ma su irin wannan tallafin daga Kannywood.


Rahama Sadau ta baiyana kudurin ta a karkashin wannan gidauniya na ciyar da mutane akalla dari biyar (500) abincin bude baki. Kuma ta bada lambar account ga ma su niyar taimako su saka kudin su na gudunmawa anan dan su gudanar da wannan yunkuri na ciyarwa.

Haka zalika ta yabawa daya daga cikin masu taimaka ma ta wajan rabon kayan abincin, wato "Zahra" ta shafin ta na instagram da facebook a yau 22 ga watan Afrilu 2021.

Leave your comment