Jaruma Daso ta shiga sahun jarumai ma su taimakon Ramadan.

Picture source :Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararriyar tsohuwar jarumar fim a Kannywood "Hajiya Saratu Gidado" da aka fi sani da "Daso" ta fara rabon abinci na tallafin watan Ramadan kamar ko wace shekara. Ta fara wannan rabon abincin bude bakin ne ga mabukata musanman almajirai da mata, dan rage mu su radadin yau da gobe da al'umma da dama su ke fama da shi a kasar nan.

Mawaki 442 ya yi kira ga masu shiga tsakanin bawa da ubangijin sa.

Tin da farkon wannan watan ne jarumar tare da ma su taimaka ma ta wajan yin girkin su ke aikin dafa abincin ga su wadan nan mabukatan. Kuma da kan ta jarumar ke raba wannan abincin.

Kawo iyanzu dai babu wani jarumi na miji daga masana'antar Kannywood da aka ga ya na rabon kayan abinci ko wani tallafi a watan Ramadan, iya matan ne kadai ake ganin taimakon su a kafafan sadarwa na zamani irin su Rahama Sadau, Hafsat Idris, Mansura Isah da kuma ita kan ta Saratu Gidado din.

Maryam Booth za ta sake fitowa a wani sabon fim na yan kudu.

Daso ta godewa daya daga cikin ma su tallafa ma ta da gudunmawan danyan kayan abinci irin su Kayan Mata da dai sauran su, kuma mabiyan ta da dama sun jinjina ma ta bisa wannan namijin kokari da take yi a duk shekara dan taimaka wa mabukata.

Leave your comment