Mawaki 442 ya yi kira ga masu shiga tsakanin bawa da ubangijin sa.

Picture source : Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen matashin mawakin zamani na salon Hausa Hip Hop da Afro Pop dan garin Zaria dake a jahar Kaduna Mr 442 ya yi jan hankali akan mutane da su ke tsegumi tare da yanke wa wasu mutanan hukunci akan abun da ya shafi tsakanin su da mahaliccin su, da su daina shiga hurumin Allah akan bayin sa. Musanman a wannan watan na Ramadan, wanda matane da dama ke komawa ga mahaliccin su dan su samu tsira da rabota a cikin watan.

Ahmad Shanawa ya Saki Sabuwar Bidiyo

Mawaki 442 ya yi kira ga masu tsegumi akan mutane da watan Ramadan, musanman yadda wadan da ake wa kallon shagalallu ne su ke shiga ta kamala tare dukufa wajan bauta wa ubangiji acikin wannan watan. Amma a gefe guda wasu su na tsagwamar wadan nan mutanan tare da zoleyar su da cewa tuban muzuru ne ba wai ya kai ga zuci ba.


Ya yi wannan kiran ne a cikin wani fefen bidiyo da ya daura a shafin sa na instagram, inda ya ke jawo ayoyin littafi mai girma tare fassara su. Ya kuma shawarci ma su irin wannan dabiyar da su kiyaye su ji da ta su rayuwar dan gudun ruguje alherin su a sanadiyar shiga tsakanin bawa da ubangijin sa.

Gidan Danger kashi na bakwai ya fito

Watan Ramadan wata ne da kowa ke kokarin nesantar duk wani abu na laifi ko zunubi dan samun rabota daga ubangijin su alfarmar watar Ramadan, dan haka babu ruwan ka da wanda kake ganin shi a shagalalle ya dawo yana sahun gaba a masallaci ko ta koma saka hijabi alhalin da matsassun kaya take sanyawa. Ruwan sa ne da Allah, babu ruwan ka kai.

Kamilu koko ya hana ni kudin da Rarara ya bashi ya bani -AleeGee

Wannan kira da 442 ya yi ga mutane ya samu goyan bayan masoyan sa da dama kuma tini su ka fara yaba masa bisa wannan kira da ya yi.

Leave your comment